logo

HAUSA

USA Today:Amurka ba ta cancanci rike ragamar dimokaradiyya ba

2021-12-13 11:07:12 CRI

USA Today:Amurka ba ta cancanci rike ragamar dimokaradiyya ba_fororder_1213-USA-Saminu

Wata makala da mujallar “USA Today” da ake wallafawa a Amurka ta fitar a baya bayan nan, ta soki lamirin jagorancin Amurka, game da kiran taron dimokaradiyya, makalar ta ce ko alama, Amurka ba ta cancanci rike ragamar dimokaradiyya ba.

Makalar ta hakaito kalaman Mr. Cliff Albright, mai rajin martaba kuri’un bakaken fatar Amurka, wanda ya taba cewa "Yayin da shugaban Amurka Joe Biden ke karbar bakuncin taron dimokaradiyya, salon mulkin dimokaradiyya a cikin gida na kara tabarbarewa. Don haka, kamata ya yi Amurka ta gyara gidanta maimakon yayata taro maras amfani”.

Kaza lika makalar ta bayyana cewa "Yunkurin da wasu bata gari cikin fushi suka yi na dakatar da zaben Amurka a ginin U.S. Capitol, alama ce dake fayyace gazawar dimokaradiyyar kasar.

Har ila yau, makalar ta ce idan har burin gwamnatin Joe Biden ita ce baiwa al’ummar duniya kariya, to dole ne Amurka ta fara nuna misali a zahiri, tare da gyara matsalolin da kasar ke fama da su.    (Saminu)