logo

HAUSA

Ka'idar Sin daya tak ita ce tsarin da kowa ya amince da ita

2021-12-10 17:09:54 CRI

Ka'idar Sin daya tak ita ce tsarin da kowa ya amince da ita_fororder_微信图片_20211210170825

Bayan da Nicaragua ta sanar da "katse huldar diflomasiyya" da mahukuntan Taiwan, kasar Sin da Nicaragua sun sanar da dawo da huldar jakadanci a tsakaninsu Jumma’ar nan. Ya zuwa yanzu, kasashe 181 na duniya, sun kulla huldar jakadanci da kasar Sin. Wannan ya tabbatar da cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce yarjejeniyar da kasashen duniya, da adalci na kasa da kasa, da ra'ayin jama'a, da kuma yanayin da kowa ya yarda da shi, kuma babu wani karfi da zai iya dakatar da wannan manufa.

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati bisa doka da ke wakiltar kasar Sin baki daya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. Wannan lamari ne na tarihi, ka'idar doka da aka amince da ita a dangantakar kasa da kasa.

A hakikanin gaskiya, duniya ta dade tana sane da cewa, "diflomasiyyar kudi" ta kasa da kasa ta hukumomin Taiwan ba wai tana kokarin taimakawa ci gaban kasashe da yankunan da abin ya shafa ba ne, sai don cimma mummunar manufar raba kasar Sin.

Idan aka kwatanta da yadda Nicaragua ta yi amfani da wannan dabi'a, hukumomin Lithuania sun yi ha'inci kan halin da ake ciki yanzu, tare da amincewa hukumomin Taiwan da su kafa wani ofishin da ake kira "Ofishin wakilci na Taiwan” a Lithuania. Wannan mataki ya saba manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za ta yabawa aya zaki. (Ibrahim Yaya)