logo

HAUSA

Malama Chen Juan: Babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macau zai bunkasa yadda ya kamata

2021-12-03 14:33:39 CRI

Malama Chen Juan: Babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macau zai bunkasa yadda ya kamata_fororder_111

An bude taron kasa da kasa game da “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina ta fito, ina kuma ta dosa—— Sauye-sauyen duniya na shekaru 100 da kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar” a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, taron da zai gudana daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan,

Wata malama dake koyar da ilimin watsa labarai a jami’ar South China University of Technology mai suna Chen Juan ta zanta da wakilin CMG, inda ta bayyana ra’ayinta cewa, bayan shekaru 30, duk wani birni a babban yankin Guangdong da Hong Kong da Macau zai sauke nauyin dake wuyansa yadda ya kamata, don kara taimakawa ci gaban yankin ta hanyar yin kirkire-kirkire. (Murtala Zhang)