logo

HAUSA

Yadda ake wanzar da dimokuradiyya a kasar Sin

2021-11-24 21:58:03 CRI

Yadda Ake Wanzar Da Dimokuradiyya A Kasar Sin_fororder_Yadda Noyan Rona ke tsoma baki cikin harkokin unguwar da yake zama (1)

A nan kasar Sin, akwai jerin wasu cibiyoyin da aka kafa a unguwannin biranen kasar, don tuntubar mazauna wurin kan harkokin kafa dokoki, cibiyoyin da suka hada da majalisar kafa dokokin kasar da ma alummar kasar, inda alumma ke iya bayyana ainihin bukatunsu da ma ba da shawarwari ga hukumar da ke kula da kafa dokoki, wadanda kuma suke taka muhimmiyar rawa wurin kafa dokoki a kasar. Bari mu dan leke wasu daga cikin cibiyoyin, don mu ga yadda suke gudana.