logo

HAUSA

Gwamnatin HKSAR ta yi kakkausar suka kan rahoton hukumar nazarin tattalin arziki da tsaro ta Amurka da Sin

2021-11-18 14:19:46 CRI

Gwamnatin HKSAR ta yi kakkausar suka kan rahoton hukumar nazarin tattalin arziki da tsaro ta Amurka da Sin_fororder_A03-HKSAR gov

Hukumar gudanarwar gwamnatin yankin musamman na Hong Kong (HKSAR), ta yi kakkausar suka da kuma nuna adawa kan jerin wasu zarge zarge marasa tushe wadanda aka bayyana cikin rahoton hukumar nazarin tattalin arziki da tsaro na Amurka da Sin wato (USCC).

Ta ce rahoton na USCC na shekarar 2021, hukumar ta ayyana wasu zarge-zarge marasa tushe kan harkokin dake shafar al’amurran Hong Kong kama daga batun dokar tabbatar da tsaron yankin Hong Kong har zuwa batun harkokin kudade da muhallin kasuwancin yankin.

A wata sanarwar da kakakin gwamnatin HKSAR ya baiwa manema labarai, gwamnatin yankin musamman ta Hong Kong ta sake yin kira ga Amurka da ta mutunta dokokin kasa da kasa da kuma muhimman dokokin dake shafar huldar kasa da kasa. Duk wani yunkuri na yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar yin katsalandan a harkokin Hong Kong ba zai taba samun nasara ba, kuma gwamnatin za ta ci gaba da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta da tabbatar da kiyaye tsaron kasa ba tare da kasala ba. (Ahmad)