logo

HAUSA

Shawarwarin da Shugaban kasar Sin ya gabatar a taron Kolin APEC na shekarar 2021

2021-11-17 08:55:14 CRI

A kwanakin baya ne, aka kammala taron kolin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik karo na 28 (APEC). Taron da bisa al’ada yake hallara shugabannin ’yan kasuwa da na gwamnatocin kasashe, inda suka tattauna manyan kalubaloli da damammaki da ake fuskanta a wannan lokaci.

Shawarwarin da Shugaban kasar Sin ya gabatar a taron Kolin APEC na shekarar 2021_fororder_211117世界21043-hoto3

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, na daya daga cikin shugabannin da suka  halarci taron ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, kuma a cikin jawabin da ya gabatar, ya yi kira da a aiwatar da kudurorin APEC na Putrajaya da gina al’ummar bai daya ta al’ummun Asiya da Pacific mai makomar bai daya, a bude kofa, mai hade dukkanin sassa, da ci gaban kirkire-kirkire, da hade dukkanin fannoni, da yin hadin gwiwar cin moriyar juna, da bunkasa hade tattalin arzikin shiyyar, da gina sahihin tsarin samar da yankin cinikayya maras shinge na Asiya da Facific cikin gaggawa.

Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi a daga martabar hadin kai maimakon yin fito na fito, a dinke maimakon rarrabuwa, da dunkulewa maimakon bin hanyoyi daban daban, da nacewa cudanyar dukkanin sassa karkashin lemar kungiyar WTO a matsayin jigo.

Shawarwarin da Shugaban kasar Sin ya gabatar a taron Kolin APEC na shekarar 2021_fororder_211117世界21043-hoto2

Ya ce, “ya dace mu maida hankali ga samar da ci gaba mai hade da kirkire-kirkire, da gabatar da alfanun fasahohin sadarwa ga karin al’ummun shiyyar Asiya da Facific. Ya kamata mu kara adadin gudummawa a fannin hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi, don tabbatar da mambobin kasashe masu tasowa sun amfana daga gare su, tare da shigar da sabon karfi ga ayyukan bunkasa ci gaba da wadatar yankin Asiya da Facific.

Xi ya kara da cewa, kasarsa za ta shiga wata sabuwar tafiya, ta gina kasa mai bin salon gurguzu na zamani. Kaza lika Sin za ta kara bude kofofinta ga duniya, tare da raba damammakin ci gabanta da sauran sassan duniya, da ma sauran kasashe dake yankin Asiya da Facific. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)