logo

HAUSA

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim: Kasar Sin dake fadada bude kofarta ga kasashen waje za ta samar da karin damammakin ci gaba ga duk duniya

2021-11-16 14:37:32 CRI

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim: Kasar Sin dake fadada bude kofarta ga kasashen waje za ta samar da karin damammakin ci gaba ga duk duniya_fororder_A

Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan nan wato Nuwamban shekara ta 2021, an gudanar da bikin CIIE karo na hudu a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, wato bikin baje-kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar, inda kamfanonin Sin da kasashen waje fiye da 1000 suka daddale yarjeniyoyin hadin-gwiwa sama da 200, wadanda darajarsu ta zarce dala biliyan 70.  

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim: Kasar Sin dake fadada bude kofarta ga kasashen waje za ta samar da karin damammakin ci gaba ga duk duniya_fororder_B

Game da ma’anar bikin na CIIE, da muhimmancin manufar da kasar Sin take aiwatarwa, na fadada bude kofarta ga kasashen waje, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, kuma shahararren masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, inda ya fara da bayyana ra’ayinsa kan muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a wajen bikin bude CIIE. (Murtala Zhang)