logo

HAUSA

Mahalartan babban taron zirga-zirga mai dorewa na kasa da kasa na MDD sun yaba wa ci gaban da Sin ta samu a fannin

2021-10-16 17:09:31 cri

Mahalartan babban taron zirga-zirga mai dorewa na kasa da kasa na MDD sun yaba wa ci gaban da Sin ta samu a fannin_fororder_src=http___inews.gtimg.com_newsapp_bt_0_12945793301_641&refer=http___inews.gtimg

Har yanzu ana gudanar da babban taron zirga-zirga mai dorewa na kasa da kasa na MDD karo na biyu a birnin Beijing, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashe sama da 170 da kungiyoyin kasa da kasa 50 ta kafar bidiyo da na zahiri. A yayin taron, bangarori daban daban da suka halarci taron sun nuna yabo ga kokarin da kasar Sin ke yi wajen raya zirga-zirga mai dorewa da ci gaban da ta samu a fannin, da kuma muhimmiyar rawar da shawarar “Ziri daya da hanya daya” wadda Sin ta gabatar kan hadewar juna a tsakanin kasashen da lamarin ya shafa ta fuskar na’urorin sufuri, da neman dauwamammen ci gaba a fannin sufuri.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce, “Ina matukar godiya ga kasar Sin sakamakon shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’ irin na juyin juya hali da ta gabatar. Wannan mataki ne mai cike da hangen nesa, yana ingiza kasashen Afirka don cimma burinsu na hadewar juna da dunkulewar nahiyar ta hanyar gina ababen more rayuwa.” (Mai fassara: Bilkisu)