logo

HAUSA

Hauhawar farashin kaya ya ragu a Najeriya a watan Satumba

2021-10-16 17:14:34 CRI

Hauhawar farashin kaya ya ragu a Najeriya a watan Satumba_fororder_430922418347835712

Alkaluman farashin bukatun kayayyaki na CPI ya nuna cewa, tashin farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu a cikin watanni shida, a yayin da adadin ya kai kashi 17.01% a watan Agusta.

Da yake bayani a taron manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Simon Harry, shugaban hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, ya danganta raguwar tashin farashin da aka samu a kasar bisa ga kwararan matakan da gwamnatin kasar ta dauka wajen daidaita al’amurra.

A cewar jami’in, gwamnatin kasar tana matukar maida hankali wajen fuskantar mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin kasar. Haka zalika, manufofin bunkasa tattalin arzikin kasa masu dorewa da gwamnati ta bullo dasu tana daukarsu da matukar muhimmanci wajen aiwatar dasu domin magance mummunan tasirin da annobar ta haifar.(Ahmad)