logo

HAUSA

Ranar Abinci ta duniya: Bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa

2021-10-16 17:19:08 CRI

Ranar Abinci ta duniya: Bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa_fororder_1074095214079377459

Ranar 16 ga watan Oktoba rana ce ta samar da abinci ta duniya. Illolin annobar COVID-19 da sauran matsaloli, sun yi matukar tasiri wajen haifar da koma bayan aikin samar da abinci a duniya, sannan kuma kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa.

kasar Sin ta sha taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta ayyukan nomansu ta hanyoyi daban daban. Tun lokacin da aka kaddamar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin hukumar inganta aikin gona da samar da abinci ta MDD wato FAO, a shekarar 1996, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tura kwararrun masana ayyukan gona da injiniyoyi kusan 1100 zuwa kasashen duniya sama da guda 40 a shiyyoyin Afrika, da Asiya, da kudancin Pacific, da yankin Caribbean da sauran sassa. Karkashin gudanarwar hukumar FAO, kwararun na kasar Sin sun yi aiki tukuru wajen daga matsayin fasahohin ayyukan noma sama da 1000 a kasashe masu yawa a fannoni daban daban na aikin noma amfanin goma, da kiwon dabbobi da halittun ruwa, da ban ruwa a gonaki, da kuma sarrafa kayan amfanin gona, lamarin da ya taimaka wajen bunkasa karuwar samar da irin shukawa a gonaki daga kaso 30% zuwa 60%. Kusan manoma 100,000 a kasashen duniya ne suka samu horon.(Ahmad)