logo

HAUSA

Mu hada kai don kare mabambantan halittu a fadin duniya

2021-10-16 18:59:02 CRI

Mu hada kai don kare mabambantan halittu a fadin duniya_fororder_78310a55b319ebc43f70666c321f50f41f1716f8

A ranar 11 ga wata ne aka kaddamar da taron na COP15 a birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan. Taken taron shi ne, "Wayewar kai game da muhallin halittu: Gina makomar bai daya ga daukacin halittun dake doron duniya", kuma dalilin da ya sa aka gudanar da taron a lardin Yunnan, shi ne sabo da irin albarkatun halittun da ake da su a wurin. Lardin Yunnan ya kasance lardin da ya fi samun mabambantan halittu a fadin kasar Sin. Domin ba da kariya ga halittun yadda ya kamata, lardin Yunnan ya tsara dokokin kare mabambantan halittu, wadanda suka sa kaso 90% na yanayin halittu da ma kaso 85% na nau’o’in halittu suka samu kariya yadda ya kamata.

Ba ma kawai a lardin Yunnan ba, a duk fadin kasar Sin ma ana ba aikin kiyaye mabambantan halittu muhimmanci. Musamman ma a cikin shekaru 10 da suka wuce, ra’ayin nan na kiyaye muhallin halittu ya yi ta shiga zukatan jama’a sosai. Bisa ga matakan da aka dauka ciki har da kafa gandun kasa, yanzu kaso 90% na yanayin halittu na kasa da ma kaso 71% na muhimman halittun da gwamnati ke kokarin kare su suna samun kariya yadda ya kamata, har ma wasu halittun da a baya suke kokarin karewa yanzu adadinsu na karuwa.

A kasance tare da mu don jin karin haske.