logo

HAUSA

‘Yan sama jannatin uku sun shiga cikin babban akwatin Tianhe yadda ya kamata

2021-10-16 16:02:58 cri

‘Yan sama jannatin uku sun shiga cikin babban akwatin Tianhe yadda ya kamata_fororder_68f88dade7834909a1a40e65bf44c5df

Bayan da kumbon Shenzhou-13 ya shiga hanyar da aka tsara a sararin samaniya, ya kuma yi nasarar hadewa da babban akwatin Tianhe. Da karfe 9:58 na safiyar ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 2021 bisa agogon Beijing, ‘yan sama jannatin uku wato su Zhai Zhigang, Wang Yaping, da Ye Guangfu sun shiga cikin babban akwatin Tianhe daya bayan daya, hakan ya nuna yadda tashar sararin samaniya ta kasar Sin ta yi maraba da rukunin ma’aikata na biyu da ‘yar sama jannati ta farko. A nan gaba, ‘yan sama jannatin za su gudanar da ayyukansu kamar yadda aka tsara. (Mai fassara: Bilkisu)