logo

HAUSA

Peng Liyuan ta halarci bikin bayar da lambar yabo ta ba da ilmi ga yara mata da mata ta UNESCO ta shekarar 2021

2021-10-15 21:46:37 cri

Bisa gayyatar da aka yi mata, uwar gidan shugaban kasar Sin, kuma manzon musamman ta UNESCO kan harkar ilimin yara mata da mata Peng Liyuan, ta halarci bikin ba da lambar yabo ta ba da ilimi kan yara mata da mata ta UNESCO ta shekarar 2021, tare kuma da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a yau Jumma’a a birnin Beijing.

A cikin jawabinta, Peng Liyuan ta bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa lambar yabo ta ba da ilimi ga yara mata da mata, bisa hadin gwiwar Sin da UNESCO a shekarar 2015, wannan lambar yabo ta ci gaba da yin tasiri mai kyau, tare da zaburar da mutane da yawa don sadaukar da kansu ga ayyukan ba da ilimi ga yara mata da mata.

A nata jawabin, Darakta Janar na UNESCO Audrey Azoulay, ta bayyana cewa, lambar yabo ta ba da ilimi ga yara mata da mata, wadda gwamnatin kasar Sin ke tallafawa, ta taka rawa ta musamman wajen taimaka wa mata da yara su cimma burinsu, musamman ma tinkarar kalubale na yaduwar annobar COVID-19.

Lambar yabo ta ba da ilimi ga yara mata da mata da kasar Sin ta kafa, tare da hadin gwiwar UNESCO, ita ce lambar yabo daya kacal ta kungiyar a fagen ingantawa, da ba da ilimi ga yara mata da mata, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen yada manufar daidaita jinsi da fasahohin da aka samu a fannin, da kuma tabbatar da manyan ayyukan kasa da kasa a fannin. (Mai fassara: Bilkisu)