logo

HAUSA

Bi da bi ne Xi Jinping ya zanta da shugaban majalissar Turai da firaministan Singapore ta wayar tarho

2021-10-15 21:56:35 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce wajibi ne Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU, su karfafa tattaunawa da juna, su kuma yi hadin gwiwar bunkasa ci gaban su cikin daidaito da lumana, matakin da ko shakka ba bu zai amfani sasan biyu.

Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a Juma’ar nan, yayin da yake zantawa ta wayar tarho da shugaban majalissar Turai Charles Michel.

A wani ci gaban kuma, shugaba Xi ya yi kira da a bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Singapore, wajen wanzar da ci gaba bayan annobar COVID-19. Shugaba Xi wanda ya yi kiran a yau Juma’a, yayin da yake zantawa ta wayar tarho da firaministan Singapore Lee Hsien Loong, ya ce ya kamata Sin da Singapore su yi aiki tare, wajen aiwatar da manufofin ci gaba bayan gushewar annobar.

Ya ce kamata ya yi sassan biyu su dora muhimmanci ga moriyar al’ummun su, tare da kara azama ga ci gaba da walwalar yankin su. Kaza lika su aiwatar da matakan wanzar da ci gaba bayan annoba, ta yadda za su kara gamsar da al’ummunsu.  (Saminu)