logo

HAUSA

Ministocin ciniki na G20 sun cimma matsaya kan zurfafa hadin kai a fannin ciniki ta yanar gizo

2021-10-14 11:12:27 CRI

Ranar 12 ga wata, an gudanar da taron ministocin ciniki na G20 a birnin Sorrento na kasar Italiya a zahiri da kuma ta kafar bidiyo. Inda aka zartas da sanarwar ministocin ciniki na G20.

Mataimakin babban direktan sashen harkokin waje na ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Chen Chao ya bayyana cewa, a yayin wannan taro, kasar Sin ta bayyana matakai masu yakini da Sin za ta dauka wajen kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban.

Bangarori daban-daban sun jaddada wajibcin zurfafa hadin kan kasa da kasa ta fuskar yakar cutar COVID-19, ban da wannan kuma, Sin ta yi alkawarin kara sulhuntawa kan manufofin ciniki da kiyaye muhalli.

Chen Chao ya ce, Sin na yanke shawarar zurfafa hadin kanta da sauran kasashe ta fuskar cinikayya ta yanar gizo, ya ce:

“Sin za ta baiwa kanana da matsakaitan kamfanoni tallafin manufofi ta fuskar yin kwaskwarima a fannin yanar gizo da shiga tsarin dake shafar bangarori daban-daban na samar da kayayyaki, don ba su goyon baya wajen samun bunkasuwa. Alal misali, ingiza bunkasuwar ba da hidima ta fuskar ciniki da kara karfin jawo hankalin jarin waje da tabbatar da yin takara cikin daidaito da kuma kara karfin ciniki ta yanar gizo da sauransu.” (Amina Xu)