logo

HAUSA

Zhao Lijian: Sin na da karfin gwiwar gudanar da gasar Olympics mai gamsarwa

2021-10-14 20:00:49 CRI

Zhao Lijian: Sin na da karfin gwiwar gudanar da gasar Olympics mai gamsarwa_fororder_下载

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar Olympic ta birnin Beijing, ta lokacin hunturu a watan Fabarairun badi. Kuma Sin na da cikakken kwarin gwiwar gudanar wa duniya da gasa mai sauki, mai tsaro kuma mai kayatarwa.

Zhao ya ce Sin na gayyatar ‘yan wasannin motsa jiki daga dukkanin kasashen duniya, zuwa gasar, domin su nuna kwarewar su a wasannin kankara da na dusar kankara.

Rahotanni na cewa, a jiya Laraba, mataimakin shugaban kwamitin kasa da kasa mai shirya gasar Olympic ko IOC, Mr. John Coates, ya kira taron manema labarai, inda ya ce IOC ba za ta matsawa kasar Sin lamba ba, dangane da shirin ta na karbar bakuncin gasar ta badi, saboda yin hakan ba ya cikin hurumin hukumar ta IOC, kuma ko kadan bai dace wata kasa ta kauracewa halartar gasar ta birnin Beijing dake tafe ba.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya ce, Sin a shirya take ta yi aiki da sassan kasa da kasa, wajen nuna adawa da siyasantar da batun wasanni, za ta kuma yi aiki tare da sassan kasa da kasa, wajen jaddada muhimmancin wasanni, karkashin kalmar "Karin hadin kai", don taimakon juna, da gudu tare a tsira tare, da kuma cimma muradun da aka sanya gaba tare. (Saminu)