logo

HAUSA

Yadda kasar Sin take kokarin kare nau’o’in halittu

2021-10-13 09:27:28 CRI

A ranar Litinin 11 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne, aka bude babban taro karo na 15 na mambobin kasashen da suka kulla yarjejeniyar kiyaye kasancewar halittu daban-daban ta duniya wato COP15 a birnin Kunming hedkwatar lardin Yunnan na kasar Sin. Sannan a ranar Talata, 12 ga wata, aka fara taron kolin shugabanni na 15 na sassan da ke halartar babban taro kan mabambantan halittu (COP15) kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron ta hanyar haɗin bidiyo.

Taken taron na wannan karo shi ne “Tabbatar da kyakkyawar makomar hallitu ta bai daya a duniya.” Yayin bikin bude taron, mataimakiyar babban darektan MDD, kana babbar darektar hukumar tsai da shirye-shiryen muhallin hallitu ta MDD Inger Andersen ta nuna cewa, kamata ya yi ko wace gwamnati da hukumomi masu zaman kansu, su ba da muhimmanci ga kiyaye muhallin halittu, ta yadda za a yi gwagwarmaya don samun kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

Yadda kasar Sin take kokarin kare nau’o’in halittu_fororder_211013世界21038-hoto4

Gabanin wannan taro ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani mai taken “Yadda kasar Sin take kare nau’o’in halittu”. Takardar ta nuna yadda har kullum kasar Sin ke dora matukar muhimmanci a kan aikin kare nau’o’in halittu, har ma ta samu gaggarumin ci gaba a wannan fanni.

Takardar ta kara da cewa, kasar Sin ta tsaya ga hada tattalin arziki da kare mabambantan halittu a gu daya, ta kuma gabatar da muhimman matakan da suka hada da kafa gandayen daji na kasa, don kare mabambantan halittu da raya ci gaban kasa ba tare da gurbata muhalli ba.

Yadda kasar Sin take kokarin kare nau’o’in halittu_fororder_211013世界21038-hoto1

Takardar ta nuna yadda kasar Sin ta sanya wannan aiki cikin shire-shiryen da ta tsara na raya sassan kasar daban daban na matsakaita da dogon lokaci, baya ga kuma inganta manufofi da dokokin da abin ya shafa, tare da inganta fasahohi da ma aikin horar da kwararru, da fadakar da al’umma kan muhimmancin aikin kare nau’o’in halittu, matakin da ya taimaka ga inganta kwarewar kasar wajen kare mabambantan halittu

Yanzu haka, akwai muhimman ni’imtattun lambunan shan iska masu damshi na kasa da kasa 64 a kasar Sin, kuma jimillar irin wadannan lambunan a duk fadin kasar ya kai 899. Yanzu kasar Sin na kara kokarin kiyayewa gami da farfado da ni’imtattun yankuna masu damshi.

Yadda kasar Sin take kokarin kare nau’o’in halittu_fororder_211013世界21038-hoto3

Daga shekara ta 2016 zuwa bara, kasar Sin ta aiwatar da ayyukan kiyayewa gami da farfado da ni’imtattun yankuna masu damshi 53, da kara gina wasu sabbin lambunan shan iska masu damshi 201, abun da ya sa muhallin halittu ya kara kyautatuwa, har ingancin ruwa ya kyautata, haka zalika yawan tsuntsaye ma ya karu sosai.

Kasar Sin dai na daya daga cikin kasashen farko da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kasancewar halittu daban-daban ta MDD. Wakilai mahalarta taron sun bayyana fatansu na ganin an tabbatar da ci gaban da aka samu a taron don amfanawa makomar Bil Adama. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)