logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a ba da tallafi ga kasashen da ke neman zaman lafiya

2021-10-13 14:16:38 CRI

Wakilin Sin ya yi kira da a ba da tallafi ga kasashen da ke neman zaman lafiya_fororder_1013-Zhang Jun-Ibrahim

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi kira da a taimakawa kasashe masu tasowa dake neman zaman lafiya, a kokarin da suke yi na tabbatar da hadin kan kasa, da samun ci gaban da ya dace, da tsayawa tsayin daka wajen nuna adawa da tsoma bakin kasashen ketare.

Zhang Jun, ya yi wannan roko ne a yayin muhawarar bainar jama’a da kwamitin sulhun MDDr ya shirya kan bambancin ra’ayi, gina kasa da neman zaman lafiya.

Jami’in na kasar Sin ya ce, bambance-bambance, dabi'a ce ta duniya. Kuma karfi na dindindin ne yake jagorantar ci gaban dan adam. Amma wani lokaci, yana iya zama tushen tashin hankali da rikici.

Zhang ya ce kasar Sin na da ra'ayin cewa, dole ne mu goyi bayan kokarin kasashe masu tasowa don kiyaye hadin kan kasa. (Ibrahim)