logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a zuba kudade domin bunkasa tattalin arzikin kasar Afghanistan

2021-10-12 09:46:14 CRI

Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a zuba kudade domin bunkasa tattalin arzikin kasar Afghanistan_fororder_1012-faiza-1-MDD

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a zuba kudade domin kare tattalin arzikin kasar Afghanistan daga durkushewa.

Antonio Guterres ya shaidawa manema labarai cewa, baya ga agajin jin kai, ya kamata kasashen duniya su dauki matakin kare tattalin arzikin kasar daga tabarbarewa.

Ya kara da cewa, bai kamata a hada batun zuba kudaden da sauran batutuwa ba, kamar amincewa ko rashin amincewa da gwamnatin kasar da kuma batun takunkumai da na haramcin da aka sanya kan kadarorin kasar. (Fa’iza Mustapha)