logo

HAUSA

Munzali Ibrahim Kabara: Ina sha’awar koyon yaren Sin!

2021-10-11 17:15:35 CRI

Munzali Ibrahim Kabara: Ina sha’awar koyon yaren Sin!_fororder_微信图片_20211011160557

Munzali Ibrahim Kabara, ko kuma Zhao Gang a yaren Sinanci, wani dan Kano ne mai shekaru 18 da haihuwa, wanda ya kwashe shekaru shida yana karantar yaren Sinanci a wata makarantar koyar da yaren Sin dake garin Kwankwaso a Kanon Najeriya.

Munzali Ibrahim Kabara: Ina sha’awar koyon yaren Sin!_fororder_微信图片_20211011160605

Duk da cewa malam Munzalin bai taba zuwa kasar Sin ba, amma yana himmatuwa sosai wajen karatun yaren kasar har yana iya magana da kuma rubutu da yaren tamkar dan kasar Sin. (Murtala Zhang)