logo

HAUSA

Jami’an Taliban da na Amurka sun tattauna kan dangantakarsu a Qatar

2021-10-10 16:53:36 CRI

Kungiyar Taliban ta Afghanistan, ta sanar da cewa, manyan jami’an gwamnatinta sun tattauna da jami’an Amurka a birnin Doha na kasar Qatar, karo na farko da aka yi irin wannan ganawa tun bayan da Amurka ta janye dakarunta daga Afghanistan a karshen watan Augusta, haka kuma ita ce tafiya ta farko da jami’an Taliban suka yi zuwa ketare tun bayan hawan mulki.

A cewar Amir Khan Muttaqi, mai rikon mukamin ministan harkokin wajen sabuwar gwamnatin Taliban, bangarorin biyu sun tattauna kan bude sabon shafi game da dangantakarsu, haka kuma jami’an Taliban sun yi kira ga Amurka ta dage haramcin da ta sanyawa kadadorin babban bankin kasar.

Ya kara da cewa, har ila yau, tawagar ta Taliban ta bukaci Amurka ta girmama cikakken ‘yancin sararin saman kasar kuma kada ta tsoma baki cikin harkokin gidanta, ana mai jaddada cewa, manufar ita ce taimakon agajin jin kai da aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da bangarorin biyu suka cimma a Doha, a watan Fabrerun 2020. (Fa’iza Mustapha)