logo

HAUSA

Yadda fasahohin zamani ke tasiri ga rayuwar bil-Adama

2021-10-06 12:05:22 CRI

A ranar 26 ga watan Satumba ne aka bude taron kolin Intanet na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 221. A sakon taya murnar da ya aike albarkacin wannan biki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce fasahohi zamani sun shafi dukkan fannonin rayuwar bil Adama kamar fannonin tattalin arziki da siyasa da al’adu da zamantakewa da makamatansu ta hanyoyin sabon tunani da sabon salo, hakan ya yi matukar tasiri ga zaman rayuwar bil Adama.

Yadda fasahohin zamani ke tasiri ga rayuwar bil-Adama_fororder_211006世界21037hoto2

Yanzu haka tattalin arzikin kasar Sin na kafofin intanet, ya karu zuwa RMB yuan triliyan 39.2, kimanin dala triliyan 6.07 a shekarar 2020, wanda ya dauki kaso 38.6 cikin dari na jimilar alkaluman tattalin arzikin kasar, inda kuma ya karu da kaso 9.7 a kan na shekarar 2019.

Wannan na kunshe ne cikin rahoton da cibiyar nazarin yanar gizo ta kasar Sin ta fitar yayin taron intanet na duniya da aka bude jiya a Wuzhen, dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin.

Yadda fasahohin zamani ke tasiri ga rayuwar bil-Adama_fororder_211006世界21037hoto4

A cewar rahoton, yawan hada-hadar kudi da aka yi ta intanet a kasar a shekarar 2020, ya kai RMB yuan triliyan 37.21, wanda ya karu da kaso 4.5 cikin dari a kan na 2019, yayin da kudin shigar bangaren cinikayya ta intanet ya kai RMB yuan triliyan 5.45, wanda ya karu da kaso 21.9 cikin dari a kan na shekarar 2019.

Rahoton ya kara da cewa, tattalin arziki na intanet ya zama babban zabi ga kasashen duniya dake neman shawo kan tasirin annobar COVID-19 domin bunkasa sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa, don haka ya zama wani sabon kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Yadda fasahohin zamani ke tasiri ga rayuwar bil-Adama_fororder_211006世界21037hoto3

Kasar Sin dai ta bayyana kudirinta na yin aiki tare da sauran kasashen duniya domin sauke nauyin neman ci gaban bil Adama tare, da raya tattalin arziki bisa fasahar intanet, da inganta aikin gwamnati da kyautata yanayin zamantakewa wajen yin amfani da bayanan intanet, da tsaron zaman al’umma bisa tsarin intanet, ta yadda fasahohin zamani, za su kawo alherai ga al’ummun kasashen duniya, da kuma raya makomar bil Adam ta bai daya. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)