logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gabatar da sabon tsarin gudanar da sufurin jiragen kasa a watan Oktoba

2021-10-02 15:39:15 CRI

Kasar Sin za ta gabatar da sabon tsarin gudanar da sufurin jiragen kasa a watan Oktoba_fororder_layin dogo

Kasar Sin za ta aiwatar da wani sabon tsarin zirga-zirgar jiragen kasa daga ranar 11 ga watan Oktoban 2021, domin kara inganta sufurin jama’a da kayayyaki.

A cewar kamfanin kula da zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin, za a inganta hidimar jiragen jigilar kayayyaki tsakanin Sin da Turai, kuma a matsakaicin mataki a kowacce rana, jiragen jigilar kayayyaki 78 za su hada birane 174 dake kasashen Turai 23, adadin da ya karu da guda 5 a kan wanda ake da shi yanzu.

Haka kuma, sama da jiragen jigilar kayayyaki 21,000 ne za su rika bin layukan dogon kasar Sin a kowacce rana.

Baya ga haka, wasu layukan dogo da dama za su fara aiki a karshen bana, inda wasu birane za su samu layukan dogo a karon farko. (Fa’iza Mustapha)