logo

HAUSA

Yadda kasashen Sin da Afirka suke bunkasa cinikayya a tsakaninsu

2021-09-29 09:07:49 CRI

A ranar Lahadi 26 ga watan Satumba ne, aka bude bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka (CAETE) karo na biyu a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.

Yadda kasashen Sin da Afirka suke bunkasa cinikayya a tsakaninsu_fororder_210929世界21036-hoto3

Bikin na daga cikin manyan matakai takwas da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka a shekarar 2018, ana gudanar da bikin ne a duk bayan shekaru biyu, kuma wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da wannan bikin, wanda a wannan karo ake saran zai gudana daga ranar 26 zuwa 29 ga wata, inda za a mai da hankali a kan hadin gwiwar sassan biyu a fannonin abinci da amfanin gona da kiwon lafiya da manyan ababen more rayuwa da hadar-hadar kudi da sauransu.

Yadda kasashen Sin da Afirka suke bunkasa cinikayya a tsakaninsu_fororder_210929世界21036-hoto2

Kamfanoni kusan 900 ne suka halarci bikin, ciki har kusan 40 wadanda suka zo daga kasashen Afirka.  Bikin na bana zai kuma nuna nasarorin da kasaahen Sin da Afirka suka cimma a fannin hadin gwiwarsu, tare da baje kolin kayayyakin da kasashen Afirka suka samar,za kuma za a yi amfani da bikin wajen kara inganta hadin gwiwar sassan biyu. Bayan kaddamar da bikin baje kolin ne kuma, aka kira taron dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar abinci da amfanin gona a karo na farko.

Yadda kasashen Sin da Afirka suke bunkasa cinikayya a tsakaninsu_fororder_210929世界21036-hoto4

A yayin taron, an shirya bikin kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwar harkokin samar da abinci da amfanin gona a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wadanda suka shafi dallar Amurka miliyan 510. Wakilai na gwamnatocin kasashen Sin da Afirka da kamfanonin da abin ya shafa sama da 250 sun halarci wannan taro。 Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta bayyana cewa, tun bayan kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, darajar cinikayya tsakanin bangarorin biyu ta karu daga yuan biliyan 87.37 a shekarar 2000, zuwa yuan triliyan 1.3 a shekarar 2020, inda a matsakaicin mataki aka samu karuwar kaso 14.5 a kowacce shekara,yawan cinikayya tsakanin kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da nahiyar Afrika, ya karu daga yuan biliyan 4.76 a shekarar 2000, zuwa yuan biliyan 783 a 2020, inda ake samun karuwar kaso 29.1 a kowacce shekara. Haka kuma jarin kamfanonin a cinikayyar dake tsakanin Sin da Afrika, ya karu daga kaso 5.4 zuwa kaso 60.2。 Wannan ya kara tabbatar da inganci da sahihancin alakar sassan biyu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)