logo

HAUSA

Meng Wanzhou Za Ta Dawo Kasar Sin Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Tsare A Canada

2021-09-25 16:40:53 CRI

Meng Wanzhou Za Ta Dawo Kasar Sin Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Tsare A Canada_fororder_huawei

Bayan shafe shekaru kusan 3 a tsare, babbar jami’ar kula da harkokin kudi na kamfanin fasaha na Huawei, Meng Wanzhou ta baro kasar Canada a jiya Juma’a, inda ta nufo gida kasar Sin.

Meng Wanzhou za ta dawo ne cikin wani jirgi da gwamnatin kasar Sin ta yi shata, inda ake sa ran isarta birnin Shenzhen da daren yau Asabar, agogon wurin.

Da take jawabi a jiyan, a lokacin da daurin talalar da aka yi mata ya kawo karshe, bayan ma’aikatar shari’a ta Amurka ta soke bukatar neman a mika mata ita, Meng Wanzhou ta bayyana godiya ga jama’a da kafafen yada labarai da gwamnatin kasar Sin da ma gwamnatin Canada.

Ta ce, cikin shekaru 3 da suka gabata, rayuwarta ta juya. Lokacin da ta bayyana a matsayin mawuyaci a gare ta kasancewarta uwa kuma mai miji kana shugabar kamfani. Amma kuma, ta ce ta kara fahimtar abubuwa da dama.

A cewarta, ba za ta taba mancewa da fatan alheri da mutane a fadin duniya suka yi mata ba. Tana mai cewa, kulabale na kara wa mutum basira.

Cikin wata sanarwa, daya daga cikin lauyoyin dake kare ta, William Taylor III, ya ce Meng Wanzhou ba ta amsa laifuffukan da ake tuhumarta ba.

Ya ce, yana farin cikin Meng da ma’aikatar shari’a ta Amurka sun cimma yarjejeniyar janye karar, kuma mai shari’a Donnelly, ta tabbatar da hakan.”

Karkashin ka’idojin yarjejeniyar, ba za a kara tuhumar Meng a Amurka ba, haka kuma, Amurkar za ta soke bukatarta na neman a mika mata Meng din. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha