logo

HAUSA

Xi Jinping: Kasar Sin ba za ta taba neman yin mulkin mallaka ba

2021-09-23 12:02:41 CRI

Xi Jinping: Kasar Sin ba za ta taba neman yin mulkin mallaka ba_fororder_0923A3推送

A yayin da yake jawabi a taron kolin MDD karo 76, shugaba Xi Jinping, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, duniya tana bukatar a tabbatar da zaman lafiya, da cigaba, da daidaito, da adalci, da demokaradiyya, da ’yanci, wadanda su ne muhimman muradun bil adama kana ya kamata a yi watsi da halayyar kafa wani karamin rukunin ’yan tsiraru, ko kuma tsarin babakere.

Kasar Sin ba ta taba kuma ba za ta taba yin danniya ko muzgunawa wasu ba, ko kuma neman yin mulkin mallaka ga sauran kasashe ba.

Xi ya ce, kasar Sin a ko da yaushe burinta shi ne gina duniya mai cike da zaman lafiya, da bayar da gudunmawa ga cigaban duniya, da kare dokokin kasa da kasa, da samar da alherai ga al’umma.

Ya kara kara da cewa, kasar Sin za ta kara kaimi wajen samar da alluran riga-kafin COVID-19 biliyan biyu ga duniya nan da karshen wannan shekarar. (Ahmad)