logo

HAUSA

Macron da Biden za su gana a Turai dangane da takaddamar sayen jiragen ruwan yaki

2021-09-23 11:25:28 CRI

Macron da Biden za su gana a Turai dangane da takaddamar sayen jiragen ruwan yaki_fororder_0923F1-nukiliya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa na Amurka Joe Biden, za su gana cikin watan Oktoba a Turai, biyo bayan tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a jiya Laraba, game da kawancen tsaro na AUKUS tsakanin kasashen Australia da Birtaniya da Amurka, .

Yarjejeniyar kawancen da Faransa ta bayyana a matsayin makarkashiya, wadda kuma ta kawo hatsaniya a Turai, ta haifar da fargaba dangane da yaduwar makaman nukiliya daga kasashen duniya, bisa la’akari da cewa a karkashin yarjejeniyar, Australia ta soke wata kwangilar sayen jiragen ruwan yaki dake zirga-zirga a karkashin teku daga Faransa domin sayen irinsu masu amfani da makamashin nukiliya daga Amurka.

Shugabannin kasashen Turai da suka fusata da matakin na Amurka, sun bayyana damuwarsu game da yarjejeniyar, inda suka bukaci bayani daga Biden kan dalilin yaudarar Faransa da sauran kasashen Turai wajen kulla sabuwar yarjejeniyar a yankin tekun Indiya da Fasifik. (Fa’iza Mustapha)