logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya manoma da masu ayyukan raya aikin gona da manoma da kauyuka murnar bikin ranar girbi ta manoman kasar Sin

2021-09-22 19:36:30 CRI

A jajibirin bikin girbin amfanin gona na manoman kasar Sin karo na hudu, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar Xi Jinping, a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar ya taya manoma da masu ayyukan raya aikin gona da manoma da kauyuka murnar bikin.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun farkon wannan shekara, Sin ta yi nasarar warware matsaloli kamar yaki da cutar COVID-19, da bala’in ambaliyar ruwa da sauransu, mun kuma samu nasarori masu tarin yawa a fannin samar da abinci da aikin gona da samun jituwa a kauyuka, da samar da rayuwa mai dadi ga manoma, wannan ya taka muhimmiyar rawa wajen yin kirkire-kirkire, da tinkarar sauye-sauye, da kuma tabbatar da yanayin da ake ciki a kasar Sin.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a farfado da kauyuka idan har ana son a farfado da dukkan al’ummar kasar. Ya kamata kwamitocin jam’iyyar JKS da gwamnatoci a matakai daban daban su dora muhimmanci ga raya aikin noma da kauyuka, da gaggauta zamanintar da su don sa kaimi ga inganta zaman rayuwar manoma. (Zainab)