logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya yi bayani game da haduwar iyalai da kaunar kasa a bikin tsakiyar lokacin kaka na Sin

2021-09-20 16:54:15 CRI

A matsayin bikin gargajiya na al’ummar kasar Sin, bikin tsakiyar lokacin kaka ya nuna burin Sinawa na haduwar iyalai da jin dadin rayuwa, tare da kaunar garinsu da ma kasarsu. Tun daga babban taron wakilan JKS karo na 18, babban sakataren jam’iyyar Xi Jinping, ya yi bayani sau da dama game da iyalai. A ganinsa, idan dukkan iyalai suka ji dadin rayuwa, hakan zai sa dukkan al’umma su samu ci gaba.

A yayin da shugaba Xi Jinping ya gana da wakilai masu halartar taron bayar da lambobin yabo ga iyalai mafi nagarta na kasar Sin na karo na farko a watan Disamba na shekarar 2016, ya bayyana cewa,“Koda lokacin da, da a yanzu, da ma nan gaba, yawancin mutane suna rayuwa a cikin iyalai, don haka ya kamata mu dora muhimmanci ga raya iyalai, da sa kaimi ga iyalai, ta yadda za su kasance tushen bunkasa kasa, da al’umma, da zamantakewar al’umma, har ma hakan ya zama mafarin cimma burin al’umma.”

A bikin gaisuwa domin murnar bikin bazara na shekarar 2017, shugaba Xi Jinping ya yi kashedi ga dukkan Sinawa da cewa, koda yake yana da kyau a yi kokari kan aiki, amma fa bai kamata a manta da iyalai ba. (Zainab)