logo

HAUSA

MDD ta mai da hankali kan aiwatar da sauye sauyen bunkasa tsarin noma

2021-09-19 17:34:07 CRI

Hukumar samar da abinci da inganta ayyukan gona ta MDD wato FAO, da asusun tallafawa ayyukan gona na kasa da kasa IFAD, da shirin samar da abinci na duniya WFP, sun yi hadin gwiwa wajen shirya bikin ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa ta MDD ta kafar intanet a ranar 17 ga watan Satumba, inda suka mayar da hankali game da tsara shirin gudanar da sauye sauyen bunkasa ayyukan noma da samar da abinci a kasashe masu tasowa domin shigar da su tsarin da kuma samun dawwamamman ci gaba.

Qu Dongyu, darakta janar na FAO, ya bayyana a cikin sakon bidiyo cewa, ana bukatar hadin gwiwar kasashe masu tasowa, da hadin gwiwar bangarori uku, da kuma hadin gwiwar kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni, don yin aiki tare wajen daidaita kalubaloli kamar matsalar karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki da aiwatar da ajandar samar da dawwamamman ci gaba nan da shekarar 2030.

Guang Defu, wakilin dindindin na kasar Sin a FAO, ya ce a matsayinta na babbar mai ba da taimako, mai shiga a dama da ita kana muhimmiyar mai bayar da gudummawa ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da hukumomin FAO, da IFAD da WFP, da sauran kasashe mambobin MDD, wajen cike gibin ci gaba a tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni, domin a samu damar cimma nasarar kawar da yunwa da talauci. (Ahmad)

Ahmad