Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya kusan kai miliyan 8.04
2021-09-14 09:40:03 CMG
Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika, ya kai 8,039,647 zuwa yammcin jiya Litinin.
A cewar cibiyar, Afrika ta Kudu da Morocco da Tunisia da Habasha na daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar.
A bangaren yawan adadin masu cutar, yankin kudanci nahiyar ne ke kan gaba, sai arewaci sai kuma yankin gabashi, yayin da yankin tsakiyar nahiyar ke da adadi mafi karanci. (Fa’iza Mustapha)