logo

HAUSA

Labarin wani likitan kasar Mauritius wanda ke kokarin tallata likitancin gargajiyar kasar Sin

2021-09-14 15:20:01 CRI

Labarin wani likitan kasar Mauritius wanda ke kokarin tallata likitancin gargajiyar kasar Sin_fororder_AA

A watan Agustar shekarar da muke ciki, an fara sayar da wani nau’in kwayar maganin mura mai suna LianHuaQingWen a kasar Mauritius dake gabashin Afirka, shi ne maganin gargajiyar kasar Sin na farko da ake sayarwa a kasar. Lamarin ba zai rasa nasaba da shigar da maganin cikin kasuwar Mauritius saboda kokarin wani likitan kasar ba, wanda ya shafe shekaru da dama yana nuna kwazo wajen tallata al’adun likitancin gargajiya na kasar Sin a Mauritius. Sunan likitan Pawan Gopaul.

Pawan Gopaul, ko kuma Lu Xing a yaren Sinanci, ya taba karatu na tsawon shekaru 9 a kasar Sin, inda ya karo ilimi sosai game da magani gami da likitancin gargajiya na kasar. Yayin da cutar numfashi ta COVID-19 ke yaduwa a kasar Mauritius a shekara ta 2020, Lu Xing ya samu labarin cewa, dabarun kasar Sin na yaki da cutar, musamman maganin kasar mai suna LianHuaQingWen na taka rawa sosai wajen hana yaduwar cutar. Don haka ya bullo da ra’ayin shigo da kwayar maganin LianHuaQingWen cikin kasarsa wato Mauritius.

“A watan Maris da Afrilun bara, yayin da cutar COVID-19 ke kara tsanani a Mauritius, na tambayi wasu malamai da abokaina, sun ambato min maganin LianHuaQingWen, inda suka ce yana da amfani sosai. Ni kuma lokacin da nake karatu a kasar Sin daga shekara ta 2009 zuwa ta 2011, na taba shan maganin yayin da na kamu da mura. Na san likitocin kasar Sin su kan baiwa mutanen da suka kamu da cutar mura ko zazzabi wannan maganin. Har ma na karanta wasu bayanai da nazarin da aka yi kan maganin, ina zaton ya dace a tallata maganin ga al’ummar Mauritius.”

Sakamakon matukar kokarin da aka yi na tsawon shekara daya, kwayar maganin kasar Sin mai suna LianHuaQingWen ya samu amincewa daga hukumomin lafiya daban-daban na kasar Mauritius a watan Agustar bana, har an fara sayar da shi a kasar, inda al’ummar kasar suke iya sayen shi cikin sauki. Jakadan kasar Sin dake Mauritius Zhu Liying ya bayyana cewa, a matsayinsa na maganin gargajiyar kasar Sin na farko da ya shiga Mauritius, fara sayar da maganin LianHuaQingWen a kasar ya bayyana hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin yaki da cutar, da samar da babban tabbaci ga al’ummar Mauritius wajen yaki da yaduwar cutar COVID-19.

Labarin wani likitan kasar Mauritius wanda ke kokarin tallata likitancin gargajiyar kasar Sin_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_1_55a19a6d-1dfc-4df5-a85f-95d3683f48c4

Ban da shi maganin gargajiyar kasar Sin, akwai sauran wasu dabarun likitancin kasar wadanda suka samu karbuwa sosai a kasar ta Mauritius, ciki har da fasahar caccaka allurai cikin sassan jikin dan Adam wato fasahar acupuncture a turance, da fasahar yin tausa. A nasa bangaren, likita Lu Xing ya kafa wata cibiyar kula da marasa lafiya a Mauritius, inda yake himmatuwa wajen tallata al’adun likitancin gargajiya na kasar Sin. Tun bayan da aka kafa shi a shekara ta 2019, cibiyar ta samu karbuwa da amincewa sosai daga al’ummar kasar. Likita Lu Xing ya bayyana cewa:

“Cibiyarmu tana samar da hidimomin jinya daban-daban bisa tsarin likitancin gargajiya na kasar Sin ga marasa lafiya, ciki har da fasahar acupuncture, da fasahar yin tausa da sauransu. Mutanen Mauritius musamman matasa suna matukar sha’awar likitancin gargajiyar kasar Sin. Akwai ma’aikata 15 a cbiyarmu, kuma kowace rana mu kan samu marasa lafiya kimanin 30 zuwa 40. Kawo yanzu akwai marasa lafiya sama da dubu 10 wadanda suka taba zuwa ganin likita a cibiyarmu, ciki har da Sinawa da yawansu ya kai kaso 2 zuwa 3 cikin dari, sama da kaso 95 bisa dari kuma al’ummar Mauritius ne. Ba mu taba tsammanin za’a samu mutane da yawa kamar haka da suka yarda da likitancin gargajiya na kasar Sin a Mauritius ba. Sun ga amfanin likitancin gargajiyar kasar Sin, daga baya za su kara gaya wa abokansu.”

Lu Xing ya ce ya gode sosai da samun damar karo ilimi a kasar Sin, saboda a nan ne ya kara fahimtar al’adun kasar musamman al’adun da suka shafi likitancin gargajiyar kasar, abun kuma da ya bude sabon babi ga rayuwarsa. Lu Xing ya kara da cewa, ya amince dari bisa dari da muhimmiyar rawar da likitancin gargajiyar kasar Sin ke takawa a fannin warkar da marasa lafiya da kyautata rayuwarsu na yau da kullum, inda ya ce:

“Na yi shekaru 9 ina karatu a China, ina matukar kaunar kasar Sin gami da al’adunta. Idan ina da zabi, ba zan zabi yin tiyata ba. A nawa ra’ayi, ya kamata a tabbatar da ingancin rayuwar marasa lafiya, wato ya kamata mu tabbatar da cewa ba za su sha wahala sosai ba lokacin da ake yi musu jinya. A ganina, likitancin gargajiya na kasar Sin na da matukar amfani, wanda ke iya yaki da cututtuka daban-daban. Likitancin gargajiya na kasar Sin tamkar wani sabon salon rayuwa ne ga al’ummar Mauritius, kuma ta hanyar karbar maganin gargajiyar kasar Sin, akwai marasa lafiyar kasar da dama wadanda suka samu sauki, ba tare da shan wahala sosai ba. Gaskiya magani gami da likitancin gargajiya na kasar Sin sun baiwa mutanen Mauritius sabon zabi.”

Lu Xing ya kara da cewa, al’adun likitancin gargajiya na kasar Sin na da makoma mai haske a Mauritius. Yana mai fatan kara kokarin tallata likitancin gargajiya na Sin, ta yadda karin kasashe da mutane za su ci moriyarsa.

Lu Xing ya ce:

“Mauritius kasa ce da ta yi suna sosai ta fannin yawon bude ido. Yawan al’ummar kasar ya zarce miliyan 1.2, kuma adadin mutanen da sukan je kasar don yawon bude ido a kowace shekara ya zarce miliyan 1.2. Mutane da dama suna son zuwa Mauritius don inganta lafiya da more rayuwarsu, kuma mun taba karbar marasa lafiya daga sauran kasashe ciki har da Madagascar wadanda suka so ganin likita. Ni zan kara himmatuwa a nan gaba, don ci gaba da raya wannan sana’a, da kara shigo da kyawawan al’adun likitancin gargajiya na kasar Sin cikin kasata wato Mauritius.” (Murtala Zhang)