Masani:Ya kamata ‘yan Afirka su magance matsalolin kasashensu da kansu
2021-09-13 15:51:48 CMG
Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kana mai lura da al’amuran kasa da kasa dake Najeriya, Dr. Mainasara Kogo Umar, ya bayyana wa wakilin CMG cewa, ya kamata ‘yan Afirka su magance matsalolin kasashensu da kansu. Masanin wanda ya bayyana haka, yayin da yake karin haske kan juyin mulkin baya-bayan nan da sojoji suka yi a kasar Guinea, ya kuma yi kira ga kasashen yammacin Afirka, da su karfafa hadin gwiwa tare da hada hannu, don taimakawa Guinea magance kalubalen da take fuskanta. (Ibrahim Yaya)