logo

HAUSA

Senegal za ta yi wa dukkan malamai da dalibai riga kafin COVID-19 kafin a koma karatu

2021-09-11 16:13:34 CMG

Senegal za ta yi wa dukkan malamai da dalibai riga kafin COVID-19 kafin a koma karatu_fororder_0911-Senegal-Faeza

Ministan lafiya na kasar Senegal, Abdoulaye Diouf Sarr, ya ce hukumomin lafiya a kasar, sun dukufa a kokarinsu na yi wa dukkan malamai da dalibai riga kafin COVID-19 kafin komawa karatu a makarantu da jami’o’i a watan Oktoba.

Ministan ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake karbar gudunmuwar riga kafi daga kasashe da hukumomin abokan hulda.

A cewarsa, gudunmuwar za ta ba su damar kara yawan wadanda za a yi wa riga kafin. Kuma dukkan yankunan kasar sun karbi na su alluran. Inda ya ce a yanzu, za su mayar da hankali ne wajen samar da wata ingantacciyar dabara yayin da za a koma karatu.

Ya ce za su tabbatar da cewa, kowanne malami da zai shiga aji, ya karbi riga kafi. Yana mai cewa wannan na da matukar muhimmanci ga dabarunsu. Baya ga haka, yayin da jami’o’i ma za su koma karatu, za a tabbatar da an yi wa dukkan dalibai riga kafi.

A cewarsa, ma’aikatarsa na hada hannu da jami’o’i da cibiyoyin karatu, domin samar da alluran da ake bukata ga dalibai. (Fa’iza Mustapha)

Faeza