logo

HAUSA

Dorewar tsagaita rikice-rikice da cimma zaman lafiya su ne tubalin sake gina kasar Libya

2021-09-11 16:29:00 CMG

Dorewar tsagaita rikice-rikice da cimma zaman lafiya su ne tubalin sake gina kasar Libya_fororder_0911-Libya-Faeza

Zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya shaidawa Kwamitin Sulhu na majalisar cewa, tsarin siyasa a kasar Libya na kan wata gaba mai muhimmanci, kuma yana fatan dukkan bangarori za su tabbatar da baban zabe a kasar, ya gudana kamar yadda aka tsara. Ya ce dorewar tsagaita rikice-rikice da cimma tsaro da kwanciyar hankali, su ne jigon sake gina kasar Libya. (Fa’iza Mustapha)

Faeza