logo

HAUSA

Zhang Chengcheng da turaren ta mai suna “Kamshi na Xi'an”

2021-08-28 14:51:54 cri

Idan da ana son gabatar da birnin Xi'an, wato wani tsohon birni dake arewa maso yammacin kasar Sin da wani kamshi ga duniya, yaya zai kasance?

Zhang Chengcheng, matashiya daga Xi'an, ta dauki kwalbar turare ta fesa cikin iska sau da yawa. Wannan kamshin dake hade da bamboo, jasmine da sandal wood nan take ya cika iska.

“Wannan shi ne turare na farko da kamfanin Guerlain na kasar Faransa ya kaddamar, wanda aka harhada bisa ruhin wani birni, kuma aka sanya masa sunan na wani birni, sunan turaren shi ne ‘Turare na Xi'an’.” Zhang Chengcheng ta bayyana haka ne cikin murmushi, tare da nuna alfahari a fuskarta.

Zhang Chengcheng da turaren ta mai suna “Kamshi na Xi'an”_fororder_张程程

A shekarar 2018, a dandalin tattaunawa kan al'adu tsakanin kasashen Sin da Faransa karo na 3, da gwamnatin birnin Xi'an na kasar Sin, da kamfanin Guerlain na kasar Faransa, sun cimma yarjejeniyar hadin kai game da nazari da kaddamar da turaren mai suna “Kamshi na Xi'an”,  tare da gudanar da bikin baje kolin gabatarwa mai taken “Shekarar Xi'an” a Turai. Bayan watanni 18 na yin kirkire-kirkire da Thierry Vasser, mai aikin harhada turare na kamfanin Guerlain ya yi, a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, an kaddamar da turaren “Kamshi na Xi'an” a hukumance a birnin na Xi'an.

Zhang Chengcheng, wadda ke da shekaru 10 tana karatu a kasar Faransa, ta yi kokarin sa kaimi kan wannan aikin hadin gwiwa na nazari, da kaddamar da turaren “Kamshi na Xi'an”.

Lokacin da take da shekaru 14, ta je birnin Metz na Faransa ita kadai domin karatu, sannan ta dawo kasar Sin bayan ta samu digiri na biyu, a wata makarantar kasuwanci ta Faransa, a yayin da take da shekaru 23. Don haka ana iya cewa, Zhang Chengcheng tabbas ta shafe shekarun kuruciyarta a kasar Faransa, kuma ta yi mamakin kwarai kan ci gaba, da canje-canje da aka samu a birnin Xi'an a duk lokacin hutu da ta koma kasar Sin a kowace shekara. Ta ce, “Ko dai an habaka sabbin yankuna, ko kuma an gina sabbin ababen more rayuwa a birnin. Ko kuma wurare masu nishadantarwa suna karuwa a kowace shekara.” Ci gaban kasar Sin ya sa ta kara yin alfahari da kasancewarta Bisiniya a lokacin da take kasar waje, kuma tana da kuduri da niyyar cewa “duk inda nake, dole ne na samu daukaka domin Sinawa”.

A cewar Zhang Chengcheng, lokacin da take karatu a jami’a, ta gano cewa, a idannun abokan karatunta masu yawa, kasar Sin tana kama da yadda ake nunawa a cikin wasu fina-finai, wato kasancewar ta wani tsohon kauye, don haka sai ta rika gayyatar abokan karatunta da su zo kasar Sin a kowace shekara don ganin ainihin kasar Sin. Zhang Chengcheng ta kara da cewa, dukkan abokan karatunta sun yi mamaki sosai bisa zamanin da kasar Sin ke kasancewa, bayan komawar su sai suka rika rubutawa a cikin rahoton kasuwanci cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan kasuwar kasar Sin.

Zhang Chengcheng da turaren ta mai suna “Kamshi na Xi'an”_fororder_张程程2

Da ta waiwayi yadda take zama da yin karatu a kasar Faransa, Zhang Chengcheng ta ce, babban tasirin da hakan ya yi gare ta, shi ne, an karfafa mutuncinta a matsayinta na ‘yar kasar Sin, kuma a sa’i guda, ra’ayi da matsayinta na kara yin mu’ammala tsakanin al’adu daban daban sun karu.”

Bayan da ta koma kasar Sin, Zhang Chengcheng ta dukufa kan ayyukan musayar al'adu tsakanin Sin da Faransa. Da farko ta kafa wata cibiyar raya al'adu ta kasa da kasa a birnin Beijing, domin shirya ayyukan musayar fasaha tsakanin matasan na Sin da Faransa, tare da hukumomin fasaha da asusun na kasar Faransa. Sannan ta kafa asusun jin kai na Shaanxi Ronghua, bayan da ta koma birnin Xi'an don ci gaba da raya ayyukan samar da hidima ga zamantakewa da musayar al'adu tsakanin su. Kasashen Sin da Faransa. Ya zuwa yanzu, asusun ya tattara kudin tallafi har Yuan miliyan 220, tare da saka Yuan miliyan 314 kan ayyukan samar da hidima ga jama'a.

Zhang Chengcheng ta ce, a cikin fiye da shekaru goma da suka gudanar da ayyukansu, sun kafa hulda mai kyau da kamfanonin Faransa da yawa, kuma kamfanin Guerlain yana daya daga cikinsu. A dandalin tattaunawar al'adu tsakanin kasashen Sin da Faransa karo na 3, an soma wani aiki game da turare mai suna “Kamshi na Xi'an” wanda ita da kamfanin Guerlain suka tsara a dogon lokaci, wanda ya sanya turaren ya zama sabon dandamalin sada zumunci a tsakanin Sin da Faransa.

Domin samun kamshin da ya fi dacewa da halayen Xi'an, Zhang Chengcheng ta raka Thierry Vasser, mai aikin harhada turare na kamfanin Guerlain, don samun tunani daga birnin Xi’an, kuma ta gayyace shi zuwa kauyen Hujiazhuang, mai nisan kilomita 40 daga Xi'an, don sanin rayuwar karkara.

Zhang Chengcheng da turaren ta mai suna “Kamshi na Xi'an”_fororder_张程程3

Kafin shekarar 2010, Hujiazhuang ya kasance sanannen kauye mai fama da talauci, wanda ya dogaro da noman alkama, masara da fita waje domin aiki, matsakaicin kudin da mazauna kauyen ke samu a kowace shekara bai wuce Yuan 1,680 kacal ba. Amma ya zuwa shekarar 2010, karkashin goyon bayan manufar “aikin gona, yankunan karkara da manoma” ta kasar Sin, da taimako daga kamfanin Zhang Chengcheng, kauyen Hujiazhuang ya samu manyan sauye-sauye, har ma yawan kudin shiga da mazauna kauyen suka samu a kowace shekara ya karu zuwa yuan 31,800.

Bayan fahimtar ci gaba da sauye sauyen da aka samu a kauyen Hujiazhuang, Thierry Vasser ba wai kawai ya yi mamaki kan saurin bunkasuwar yankunan karkara na kasar Sin ba ne, har ma ya yaba da kokarin da Sinawa suke yi.

Bayan bincike da aka yi, a shekarar 2019, kamfanin Zhang Chengcheng da na Guerlain, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya, don habaka wani sansanin shuke-shuken kayan kamshi sama da kadada 200 a kauyen Hujiazhuang. Bisa ma’aunin kamfanin Guerlain ne kuma aka dasa tsirrai masu kamshi, don kara fadada hanyar inganta masana'antar aikin gona, da kara jin dadin rayuwar mazauna kauyen.

Tun daga wannan lokacin, turaren “Kamshi na Xi'an” ya wuce samfur ko alamar al'adu kadai, inda ya zama yana da alaka da mutanen da ke zaune a wannan yankin. Kamar yadda Zhang Chengcheng ta fada, “A ko da yaushe burina shi ne kara inganta garinmu, zuwa wani dandalin duniya mai girma.”