Sin ta jaddada adawar ta da tsoma bakin Amurka cikin harkokin yankin Hong Kong
2021-08-09 09:56:28 CRI
Ofishin wakilci na majalissar gudanarwar kasar Sin game da harkokin Hong Kong da Macao, ya yi matukar suka kan matakin Amurka na tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, da ma sauran batutuwan da suka shafi cikin gidan kasar Sin.
Kakakin ofishin ya yi kakkausan suka ga matakin na Amurka a jiya Lahadi, cikin wata sanarwa mai kunshe da martani, ga wata takardar sanarwa da gwamnatin Amurka ta fitar kan batun yankin Hong Kong.
Kakakin ya ce, ikirarin Amurka cewa wai tana tare da al’ummun yankin Hong Kong, ba komai yake nufi ba, illa goyon bayan tsirarun mutane dake adawa da kasar Sin, wadanda ke son hargitsa yanayin zaman lafiya a Hong Kong.
Ya ce gwamnatin Amurka na son haifar da wani yanayi ne na rashin zaman lafiya a Hong Kong, tana kuma fatan masu rajin nuna adawa da Sin za su ci gaba da aiwatar da munanan manufofin su.
Jami’in ya kara da cewa, ta hanyar daukar nauyin kungiyoyin masu nasaba da Hong Kong, da kaddamar da kudurorin doka, da matakan gwamnati, Amurka na fatan wargaza Hong Kong tare da muzgunawa kasar Sin, a maimakon kare dimokaradiyya, da ‘yancin bil adama, ko martaba ka’idar nan ta kasa daya tsarin mulki biyu, kamar yadda Amurkan ke ikirarin tana yi. (Saminu)