logo

HAUSA

Mu leka birnin Quanzhou

2021-08-06 21:38:21 CRI

Mu leka birnin Quanzhou_fororder_fcfaaf51f3deb48f6b0ca6c2630adc212df57867

A ranar 1 ga wata, aka rufe taron kwamitin kula da wuraren gado na hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya aladu na MDD UNESCO a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian na gabashin kasar Sin, inda aka kara wasu sabbin wurare 34 cikin jerin wuraren gado na duniya.

Sabbin wuraren da suka hada da wuraren aladu 29 da na halitta 5, wadanda suka kawo adadin irin wadannan wurare a duniya zuwa 1,154.

Daga cikin sabbin wuraren, akwai “Quanzhou: cibiyar cinikayya ta ruwa ta duniya, tsakanin daular Song da Yuan” dake lardin Fujian, wanda ya kawo adadin irin wadannan wurare a kasar Sin zuwa 56.

A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske dangane da birnin na Quanzhou.(Lubabatu)