Xi Jinping da takwaransa na Saliyo sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu
2021-07-29 14:27:09 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Saliyo Julius Maada Bio, sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, yayin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho.
A lokacin zantawar tasu, Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, tun bayan kafuwar huldar diplomasiyya tsakaninsu, kasashen biyu sun dade suna goyon baya juna, da fahimtar juna kan batutuwan dake shafar muradunsu masu tushe, da wasu manyan batutuwan dake jawo hankalinsu, da kuma samun ci gaba mai armashi, dangane da hadin kansu a fannin zamantakewar al’umma da tattalin arziki.
Game da batun tinkarar cutar COVID-19 kuwa, jama’ar Sin da Saliyo sun kara hadin gwiwarsu, matakin da ya bayyana dankon zumuncin dake tsakaninsu. Ya kuma jaddada cewa, yana fatan za a yi amfani da zarafi mai kyau, na cika shekaru 50 da kafuwar huldar sassan 2, don inganta zumunci, da kara amincewa da juna, da zurfafa hadin gwiwa da kuma ingiza bunkasuwar dangantaka abota bisa tsare-tsare a duk fannoni, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu da jama’arsu.
A nasa bangare, Julius Maada Bio, ya bayyana fatansa na kara hadin kai da kasar Sin, don inganta zumunci a tsakaninsu, da zurfafa hadin kansu a fannoni daban-daban.
Ban da wannan kuma, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bugawa takwaransa na kasar David Francis wayar tarho, don taya juna murna kan wannan batu. (Amina Xu)