logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku don daidaita bambancin ra’ayi dake tsakanin kasashen Sin da Amurka

2021-07-28 09:01:29 CRI

A wannan makon ne, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya gana da mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka Wendy Sherman a birnin Tianjin, inda ya sanar da cewa, alakar Sin da Amurka ta gamu da cikas, sakamakon yadda wasu Amurkawa ke yayata Sin a matsayin abokiyar gaba. Yana mai cewa, lokaci ya yi da Amurka za ta yi watsi da wannan mummunan tunani, da manufofi masu hadarin gaske.

Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku don daidaita bambancin ra’ayi dake tsakanin kasashen Sin da Amurka_fororder_210728世界21028-hoto2

Xie ya ce, Amurka na aiwatar da manufofi uku masu hadari, wato takara, da hadin gwiwa da fito na fito, wadanda babban makasudinsu shi ne dakile kasar Sin. Amurka na fatan fito na fito da kasar Sin zai ba ta damar cimma babban burinta, yayin da hadin gwiwa zai saukaka mata cimma nasara, kana takara ta zame mata tarko da take amfani da shi wajen haifar da hargitsi.

Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku don daidaita bambancin ra’ayi dake tsakanin kasashen Sin da Amurka_fororder_210728世界21028-hoto3

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, idan Amurka na fatan yin hadin gwiwa da Sin yadda ya kamata, ya dace ta yi hakan bisa gaskiya da kuma martaba ’yanci da muradu da cikakkun yankunanta. Ta kuma yi amfani da sassa da take da fifiko cikin su, wajen inganta shigar da hajoji, da kawar da takunkumin cinikayya. Ta kuma daina yin amfani da rikici ko yin fito na fito wajen dakile ci gaban kasar Sin.

Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku don daidaita bambancin ra’ayi dake tsakanin kasashen Sin da Amurka_fororder_210728世界21028-hoto4

Sanin kowa ne cewa, Amurka tana mayar da kanta a matsayin ’yar sandar duniya, inda take yunkurin mayar da dokoki da ka’idojinta na gida, da na wasu tsirarun kasashen yamma a matsayin dokokin kasa da kasa, tare da kullewa da darkushe sauran kasashe. Kaza lika suna dagewa wajen tankwara ka’idojin sauran sassa, da yunkurin cimma gajiyar kashin kai. A hannu guda kuma, suna son rungumar salon danniya, ta yadda masu karfi za su farauci marasa karfi, kuma manya za su ci zalin kanana.

Bayanin gabatarwa a tattaunawar da kasashen Sin da Amurka suka yi ta fayyace komai ba tare da wata rufa-rufa ba, an kuma karfafa fahimtar matsayin kowane bangare, yayin da tattaunawa da gaba, za ta karkata ga bunkasa hadin gwiwa mai tsafta tsakanin kasashen biyu. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)