logo

HAUSA

MDD ta yi kira ga shugabancin G20 ya dauki mataki game da sauyin yanayi

2021-07-26 11:11:53 CRI

MDD ta yi kira ga shugabancin G20 ya dauki mataki game da sauyin yanayi_fororder_210726-UN chief-Fa'iza

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya yi kira ga shugabancin kungiyar G20 da ya dauki mataki kan matsalar sauyin yanayi.

Da yake jawabi ga taron ministocin kungiyar G20 kan muhalli da yanayi da makamashi, Antonio Guterres ya ce duniya na bukatar dukkan kasashe su gaggauta cimma burin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, na rage dumamar yanayi zuwa digiri 1.5 ba tare da wani tsaiko ba. Yana mai cewa ba yadda za a cimma wannan buri ba tare da shugabancin G20 ba.

Ya ce wannan abu ne da biliyoyin mutane da kasuwanni da masu zuba jari da masana’antu dake fuskantar tasirin sauyin yanayi ke bukata, domin tabbatar da cewa, ba makawa za a daidaita yawan hayaki mai guba da ake fitarwa da kuma abubuwan da za su shawo kansu a nan gaba.

Yayin da ya rage kwanaki 100 kafin gudanar da taron MDD kan sauyin yanayi a Glasgow na Scotland, Sakatare Janar din ya bukaci kasashen G20 da sauran shugabannin, su dage wajen cimma burin daidaita hayakin da ake fitarwa zuwa tsakiyar karnin da gabatar da ingantattun tsaruka tunkarar yanayi na kasa da aiwatar da dabaru masu karfi da matakan da suka dace na cimma burin, ciki har da kaucewa sabon makamashin Kwala bayan 2021 da soke rarar man fetur da amincewa mafi karancin farashin sinadarin Carbon, kamar yadda asusun IMF ya bayar da shawara.

Haka kuma, ya ce ya kamata kungiyar kasashe 7 da sauran kasashen da masu karfi, su tallafawa kasashe masu tasowa, ciki har da cimma burin samar da dala biliyan 100 da kara yawan tallafi zuwa a kalla kaso 50 kan kudaden tunkarar yanayi da kuma sanya bankuna daban-daban daidaita manufofinsu ta yadda za su dace da bukatun kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)