logo

HAUSA

Sin ta bukaci a dauki matakin gaggawa na koli kan yanayi mai tsanani

2021-07-26 20:31:55 CRI

Hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin, ta yi kira da a dauki matakin gaggawa na koli, yayin da ake tunkarar matsanancin yanayi, da kare muhimman kayayyakin more rayuwa dake yankunan birane.

Hukumar wadda ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar Litinin din, ta kuma bayyana cewa, kamata ya yi a inganta shirye-shiryen tunkarar yanayin mai tsanani, da hanzarta daukar matakai. Yanzu haka kasar Sin na fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya da mahaukaciyar guguwa mai tafe ruwa da iska suke barna a sassan kasar da dama, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da tattalin arziki.(Ibrahim)