logo

HAUSA

Masar ta karbi bakuncin horon bunkasa hadin gwiwa a fannin sararin samaniya tsakanin kasashen Afrika

2021-07-26 10:15:03 CRI

Masar ta karbi bakuncin horon bunkasa hadin gwiwa a fannin sararin samaniya tsakanin kasashen Afrika_fororder_210726Egypt-Fa'iza

Hukumar kula da sararin samaniya ta Masar EgSA, ta kaddamar da horon fasahohi ga injiniyoyi da kwararru 17 daga kasashen Afrika 5, domin bunkasa hadin gwiwa da musaya a fannin sararin samaniya.

Horon na kwanaki 12 da zai gudana har zuwa 5 ga watan Augusta, zai kunshi rubutattun darussa da kuma wanda za a yi a aikace, da nufin horar da jami’ai daga kasashen Nijeriya da Sudan da Ghana da Uganda da kuma Kenya.

Yayin bikin bude horon, shugaban hukumar EgSA, Mohammed El-Koosy, ya shaidawa mahalartan cewa, samar da fasahar da ta shafi sararin samaniya ba abu ne mai sauki ba, saboda yana bukatar gogewa da kuma kudi. Amma kuma ba abu ne da ba zai yuwu ba, domin za a iya aiwatarwa ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika a fannin ayyukan da suka shafi sararin samaniya wadanda ke da tasiri ga tattatlin arzikinsu da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Bayan budewar, baki da ma masu karbar horon sun yi rangadi a cibiyar hada tauraron dan Adam da gwaji wato (AITC) dake karkashin hukumar EgSA, wadda ake ginawa da taimakon kasar Sin.

Mohammed El-Kossy ya kuma yabawa taimakon da Sin ke ba Masar a fannin ayyukan sararin samaniya da ma tallafin da ta bayar na kafa cibiyar AITC da tauraron MisrSat II da ake iya sarrafawa daga nesa, yana mai cewa kwararrun Sinawa za su horar da ma’aikatan EgSA, kafin su mika ragamar cibiyar ga kasar.

Da yake tsokaci, darakta janar na hukumar rayawa da binciken sararin samaniya ta Nijeriya, Halilu Ahmed, ya ce ya zama wajibi a hada hannu wajen kai nahiyar Afrika matakin da ake buri. Yana mai cewa, hakkinsu ne su raya kimiyya da fasaha, kuma hukumar kula da sararin samaniya ta Masar ta zama jagora a wannan fanni. (Fa’iza Mustapha)