logo

HAUSA

Sin: Me ya sa Amurka ta mai da kanta a matsayin abin koyi a fannin demokuradiyya da kare hakkin Bil Adama

2021-07-26 13:55:30 CRI

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya gana da takwararsa ta kasar Amurka Wendy Sherman, a birnin Tianjin na kasar Sin, inda ya nuna cewa, ya kamata Amurka ta daidaita matsalarta game da kare hakkin Bil Adama da farko. Ya ce idan an duba tarihi, a da can Amurka ta yi kisan gilla kan mazauna asalin kasar, a wani bangare na daban kuma a yanzu, Amurkawa kimanin dubu 620 sun mutu sakamakon gaza daukar matakan yakar cutar COVID-19.

Ban da wannan kuma, Amurka ta baza jita-jita don tayar da yake-yake, matakin da ya haifar da barazara matuka ga jama’ar duniya. Amma shi duk da hakan, me ya ba Amurka ke da kwarin gwiwar zama abun koyi a duniya, ta fuskar demokuradiyya da kare hakkin Bil Adama?

Xie Feng ya ce, Amurka ba ta cancanci ta tsoma baki cikin harkokin kare hakkin Bil Adama, da demokuradiyya ga kasar Sin ba. Ganin yadda Sinawa ke bayyana karfin kirkire-kirkire, da samar da kayayyaki karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma nagartattun matakan siyasa da take aiwatarwa, da hanyar bunkasuwa dake dacewa da halin da Sin ke ciki. Shin ko jama’a da ba su da demokuradiyya da ‘yanci da hakkinsu, suna iya cimma nasarorin a zo a gani kamar haka? Shin ko kasar dake da yawan mutane da ya kai fiye da biliya 1 tana iya samun saurin bunkasuwsar tattalin arziki da al’umma cikin dogon lokaci?

A wani sakamakon nazarin jin ra’ayin jama’a da wasu kasashen yamma suka gudanar, yawan Sinawa da suke bayyana amincewa, da gamsuwa ga gwamnatin Sin ya kai kaso 90%, wanda hakan ya zama abu mai ban mamaki da ya faru a wata kasa.

Ban da wannan kuma, Xie Feng ya ce, Sin na fatan kasashen biyu za su nuna wa juna daidaito, da fahimtar bambancin dake tsakaninsu. Dole ne kuma Amurka ta karkata matsayin da ta dauka, don zabar hanyar da ta dace game da dangantakarta da kasar Sin, da mutunta juna, da yin takara bisa adalci, da zama tare cikin lumana.

Bugu da kari, dangantakar kasashen biyu mai dorewa, na dace da muradun kasashen biyu, wadda ke biyan bukatun daukacin al’ummar duniya, a cewar Xie Feng. (Amina Xu)