logo

HAUSA

Africa CDC: Yawan masu kamuwa da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 6.41

2021-07-25 17:26:12 CRI

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce ya zuwa ranar Asabar, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 6,415,413.

Afrika CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU ta ce, adadin mutanen da cutar ta kashe a nahiyar ya kai 162,875, yayin da yawan mutanen da suka warke daga cutar ya kai 5,630,564 a duk fadin nahiyar.

A cewar Afrika CDC, Afrika ta kudu, Morocco, Tunisia, Masar da Habasha, su ne kasashen da suka fi yawan masu kamuwa da cutar a nahiyar.

Afrika ta kudu ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 a Afrika, inda take da adadin mutane 2,356,049 da suka kamu da cutar, yayin da kasar Morocco dake arewacin Afrika ke bi mata baya, tana da adadin mutane 569,668 da aka tabbatar sun kamu da cutar, ya zuwa ranar Asabar.

Game da adadin yawan masu kamuwa da cutar kuwa, shiyyar kudancin Afrika ne ke sahun gaba a matsayin yankin da annobar ta fi shafa, sai arewaci da gabashin Afrika dake bi mata baya a nahiyar, shiyyar Afrika ta tsakiya ne ke da karancin masu kamuwa da cutar a nahiyar, kamar yadda Afrika CDC ta bayyana.(Ahmad)