logo

HAUSA

Afirka ta Kudu ta gamu da yanayin sanyi mai tsanani

2021-07-25 17:19:15 CRI

Afirka ta Kudu ta gamu da yanayin sanyi mai tsanani_fororder_bffac4e2da4a41d78cf0c134e66acff3

Bisa sanarwar da hukumar hasashen yanayi ta kasar Afirka ta Kudu ta bayar a daren ranar 23 ga wata, an ce, an samu yanayin sanyi mai tsanani a kasar, kana yanayin zafin wurare da dama a kasar ya sauka wanda ya karya matsayin bajinta a bisa tarihin yanayin sanyi na kasar.

Hukumar ta bayyana cewa, ana samun kankara a wurare da dama a kasar, yanayin zafin wuraren ya ragu sosai ba zato ba tsammani a cikin awoyi 24 da suka gabata, inda aka samu barkewar yanayin sanyin a wurare 19 mafi tsanani a tarihin kasar, daga cikin wuraren, yankin Kimberley dake jihar arewacin Cape Town ya fi gamuwa da yanayin sanyi mafi tsanani, wato ma’aunin yanayi na yankin ya sauka zuwa maki 9.9 kasa da sifiri. An ce, za a ci gaba da fuskantar yanayin sanyi mai tsanani har na tsawon kwana daya ko biyu, an yi hasashe cewa, za a samu farfadowar dumi sannu a hankali tun daga ranar 26 ga wannan wata. (Zainab)