logo

HAUSA

Shugaban AU ya jaddada aniyar kafa kasashe biyu a matsayin hanyar warware batun Israel-Palestine

2021-07-25 15:20:26 CRI

Moussa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, ya sake yin kira da a warware batun Isra’ila da Falastinu ta hanyar kafa kasashe biyu masu ‘yancin gashin kai, kamar yadda aka bayyana cikin sanarwar AU.

A cewar sanarwar, shugaban na AU ya yi tsokaci a ranar Alhamis din da ta gabata a yayin tattaunawa da jakadan Isra’ila a kasar Habasha Aleli Admasu, inda bangarorin biyu suka tattauna game rikicin Isra’ila da Falastinu wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Shugaban na AU ya ce rikicin wanda aka shafe sama da shekaru 70, inda masu shiga tsakani na shiyyoyi da na kasa da kasa suke ta kokarin lalibo hanyoyin warware takaddamar tsakanin bangarprin biyu.

A cewar Mahamat, ba iya hanyar da za ta tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali daga dadadden rikicin kadai ya kamata a bi ba, har ma ya dace a tabbatar da kare hakkokin kowane bangare.

Ya ce kungiyar ta Afrika, a cikin shekaru kusan sittin a tarihin kafuwarta, ta sha nanata aniyarta game da batutuwan dake shafar rikicin Falastinawa da Isra’ila cewa, kafa kasashe biyu masu cin gashin kai ita ce sahihiyar hanyar da za ta tabbatar warware rikicin da kuma samun dorewar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.(Ahmad)