logo

HAUSA

Kasar Sin ta kuduri aniyar sanya takunkumi kan wasu ‘yan Amurka gami da hukumomin kasar 7

2021-07-24 16:47:57 CRI

Kasar Sin ta kuduri aniyar sanya takunkumi kan wasu ‘yan Amurka gami da hukumomin kasar 7_fororder_AA

A baya-bayan nan ne ma’aikatar harkokin waje, da ma’aikatar kudi, da ma’aikatar kasuwanci, gami da ma’aikatar tsaron kasa ta Amurka, suka yi gargadi kan harkokin kasuwancin Hong Kong. Kana, ofishin kula da jarin waje na ma’aikatar kudin Amurka ya sanya takunkumin tattalin arziki kan wasu mataimakan daraktoci 7 na ofishin tuntuba na kwamitin tsakiya na gwamnatin jama’ar kasar Sin a Hong Kong. A don haka, kasar Sin ta ce za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba don kare iko da moriyarta na samar da ci gaba. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya ce, kasarsa ta kuduri aniyar sanya takunkumi kan wasu Amurkawa gami da hukumomin kasar 7.

Kakakin ya ce, Amurka ta yi gargadi kan harkokin kasuwancin Hong Kong, da shafawa yanayin kasuwancin Hong Kong bakin fenti, tare kuma da sanya takunkumi ba bisa doka ba kan jami’an gwamnatin kasar Sin da dama dake wajen, al’amarin da ya sabawa dokokin kasa da kasa gami da muhimman ka’idojin dangantakar kasa da kasa, tare da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Kuma dukkansu abubuwa ne da kasar Sin ke adawa da su tare da yin Allah wadai.

Kakakin ya kara da cewa, domin mayar da martani kan abun da Amurka ta yi, kasar Sin ta kudiri aniyar sanya takunkumi kan wasu mutane gami da hukumomin kasar 7, ciki har da tsohon sakataren kula da harkokin kasuwancin Amurka Wilbur Louis Ross, da shugabar kwamitin tantance tattalin arziki da tsaro na Amurka da Sin na majalisar dokokin kasar wato USCC a takaice Carolyn Bartholomew, da shugaban hukumar bibiyar yanayin kare hakkokin jama’a da dokoki a kasar Sin ta Amurka, Jonathan Stivers, da DoYun Kim daga kungiyar demokuradiyya ta harkokin kasa da kasa ta Amurka, da babban jami’in shirye-shirye na cibiyar dake rajin tabbatar da ‘yanci da demokuradiyya a duniya ta Amurka, da darektar kula da harkokin kasar Sin ta kungiyar dake rajin kare hakkin dan Adam mai suna Human Rights Watch Sophie Richardson, gami da kwamitin demokuradiyya na Hong Kong. (Murtala Zhang)