logo

HAUSA

Sin ta yi tir da matakin Japan da Amurka na sukar manufofinta

2021-07-22 20:58:54 CRI

Sin ta yi tir da matakin Japan da Amurka na sukar manufofinta_fororder_赵立坚

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ta gabatar da korafi game da matakin da kasashen Japan da Amurka suka dauka, na sukar manufofinta na cikin gida.

Rahotanni sun hakaito yadda shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen Japan, ya fitar da wata sanarwa a ranar Talata, game da tattaunawar da babban mataimakin ministan wajen kasar Takeo Mori, da mataimakin babban sakataren wajen Amurka Wendy Sherman suka yi, inda suka soki Sin game da batutuwan da suka shafi tekun gabashi da kudancin kasar. Kaza lika sassan biyu sun jaddada abun da suka kira, bukatar wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin Taiwan, tare da nuna damuwa da halin da jihar Xinjiang da yankin Hong Kong na Sin ke ciki.

Game da hakan, Zhao Lijian ya jaddada cewa, dukkanin batutuwa da suka shafi yankin Taiwan, da Hong Kong da Xinjiang, harkoki ne na cikin gidan Sin, wadanda ba sa bukatar tsoma bakin wasu sassan waje.

Zhao Lijian ya shaidawa taron manema labarai cewa, kar wani ya raina ikon kasar Sin na kare ‘yancin mulkin kai da tsaron yankunan ta. Kuma duk wani nau’in tsoma baki cikin batun da ya shafi tekun gabashi da kudancin Sin, zai haifar illa, tare da gurgunta moriyar kasashen dake yankin. (Saminu)