logo

HAUSA

Liu Guizhen: Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan aka yi kokarin taimakawa sauran mutane

2021-07-05 20:28:36 CRI

Liu Guizhen: Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan aka yi kokarin taimakawa sauran mutane_fororder_Liu Guizhen1

Liu Guizhen, wata mambar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ce a gundumar Daixian ta birnin Xinzhou dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin. Ta rike mukaman da suka hada da shugabar reshen jam’iyya a kauye, daraktar kwamitin kauye, kuma malama, haka kuma likita a cikin shekaru 40 da suka gabata. Liu ta taba tambayar mahaifinta abun da ya kamata ta yi don zama cikakkiyar ‘yar jam’iyya. Inda ya ba ta amsa da cewa, “ki rika tunanin sauran jama’a a zuciyarki, kuma ki yi iya kokarinki wajen taimaka musu”. Kuma wannan ya kasance burin da uban da ‘yarsa suka sanya gaba.

Taron da ake a garin dake makwabta da su zai kare da tsakar rana. Kuma ana kammalawa, Liu Guizhen ta gaggauta komawa kauyensu don tattauna batun kyautata muhalli da sauran mambobi. Bayan nan, ta taimaka wajen auna yanayin hawan jinin sauran mutanen kauyen. Daga irin wadannan ayyuka, mutum zai iya gane yanayin rayuwar Liu mai cike da hada-hada.

An haifi Liu Guizhen a Duanjiawan, wani karamin kauyen dake kusa da tsaunin Nanshan dake gundumar Daixian. Mahaifinta Liu Baixiao, ya shiga JKS ne a shekarar 1943, kuma ya zama sakataren reshen jam’iyyar na farko dake kauyen ne a shekarar 1946.

“Ke kadai ce kika yi babbar sakandare. Wa kike tsammanin zai yi ayyukan?” abun da Liu Baixiao ya taba tambayar ‘yarsa ke nan.

Kalaman mahaifinta sun zaburar da ita wajen daukar nauye-nauye. Liu Guizhen ta hakura da damar da ta samu na shiga jami’a, kuma a 1978 ta zama likitar kauye, domin ta kula da al’umma.

Shekaru 10 bayan nan, aka sauyawa malami daya tilo na kauyen wajen aiki.

“Kawai ki rika koyarwa kafin sabon malami ya zo. Ba za a jima ba”, cewar mahaifinta. Bisa kwarin gwiwar da ta samu daga mahaifinta, Liu ta kara daukar nauyin zama malama.

A 1996, aka zabi Liu Guizhen a matsayin sakatariyar reshen jam’iyya na kauyen. A shekarar 2003 kuma aka zabe ta matsayin daraktar kwamitin kauye.

Liu Guizhen: Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan aka yi kokarin taimakawa sauran mutane_fororder_Liu Guizhen2

A baya, mazauna kauyen kan je asibiti ne idan ba su da wata mafita, saboda ba za su iya biyan kudin asibitin ba. Samun Likita a kauyen, dadadden burin bai daya ne na al’ummar.

Bisa la’akari da wannan yanayi, Liu Guizhen ta tafi birni, ta karanci fannin likitanci. Rabin shekara bayan nan, ta kammala karatunta ta koma kauyen, inda ta fara duba marasa lafiya.

A shekarun da suka biyo baya kuma, ta mayar da hankali wajen gudanar da bincike, inda kwarewarta na aikin likitanci ya inganta. Ta koyawa kanta yadda ake acupuncture kuma tana yawan amfani da wannan dabara ta likitancin gargajiya na kasar Sin domin kula da marasa lafiya a kyauta. Wani lokacin ma da kudinta take sayawa mutane masu bukata magani.

A wani lokaci, wani mara lafiya mai suna Chen Zhiliang, ya kashe kudin da ya kai sama da yuan 30,000 kwatankwacin dala 4,607 a asibiti, lamarin da ya haifar da matsin rayuwa ga iyalinsa. Sai Liu Guizhen ta taimakawa Chen, inda aka mayar masa da kudinsa karkashin shirin inshorar lafiya na hadin kai na kauyen.

Tsarin inshorar lafiya na kauye da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar a 2003, na da nufin tabbatar da cewa mazauna kauyuka na samun hidimomin kiwon lafiya ba tare da sun kashe kudadensu ba. Da farko, galibin mutanen kauyen sun ki biyan kudin da ake bukata na shiga inshorar. Don haka, Liu ta yi amfani da kudinta wajen biyawa wasu daga cikinsu. Amma bayan an mayarwa Chen kudin da ya kashe a asibiti, sai karin mutane suka shiga shirin.

Mazauna kauyukan dake kewaye da su, sun bukaci ta rika duba iyalansu. Tazarar dake tsakanin gidan Liu Guizhen da kauye mafi nisa ya kai sama da kilomita 5. A baya, babu tituna masu kyau da kekuna za su bi cikin sauki, don haka, sai ta bi hanyoyin dake cike da tsaunika. Wani lokaci, ta kan kwana a gidajen marasa lafiya saboda ta yi dare.

“Na koyi dabarun da suke da amfani ga mutane, don haka ina son zama mai hidimta musu”, cewar Liu Guizhen.

A shekarar 1998, malami daya tilo na kauyen ya tafi. Saboda nisan kauyen da rashin kyan muhalli, wasu malamai ba sa son zuwa. Sai iyaye suka fara damuwa da dakatarwar da aka yi na karatu. A nan ma, sai Liu Guizhen ta cike gurbin da aka samu.

Ta mayar da gidanta zuwa aji a lokacin da ake sake fasalin makarantar, kuma ta yi amfani da duk wani abu da za ta iya, ciki har da teburi da gado da allo, domin koyarwa da daliban.

An kammala ginin makarantar a kan lokaci domin fara sabon zangon karatu. Sai dai, kauyen bai samu damar daukar sabon malami ba. Liu Guizhen ta ci gaba da cike wannan gurbi. Ta koyar da harshen Sinanci da lissafi da kimiyya da sauran wasu darussa ga daliban dake aji 1 zuwa 5.

A shekarar 2006, aka samu sabon malamin da zai yi aiki a makarantar firamare. Sai dai kuma an samu karin dalibai, lamarin da ya kai ga bukatar malamai biyu. Don haka, Liu Guizhen ta sake daukar wannan nauyi.

Ta kan sayi kayayyaki kamar toilet paper da fensira, ga yaran da suke bukata. Saboda kokarinta, babu wani dabili da ya daina zuwa makaranta. Da yawa daga cikin dalibanta sun kammala makarantar midil, yayin da wasu kuma suka shiga Jami’a.

“Na gaza shiga jami’a,” cewar Liu Guizhen. “yaran sun taimaka min cimma burina.”

Liu Guizhen: Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan aka yi kokarin taimakawa sauran mutane_fororder_Liu Guizhen3

Ban da wannan kuma, Liu Guizhen ta kan yi tafiye-tafiye akai-akai zuwa wasu yankuna domin nazartar yanayin da suke ciki, ta yadda za ta iya taimaka musu samun karin kudin shiga.

Bisa la’akari da yanayin shimfidar yankin, da sauran wasu batutuwa, Liu Guizhen ta yanke shawarar tattara jama’a domin noman itacen Pinus Tabulaeformis a bakin kogi.

“Da farko, mutanen kauyen na tsoron yin asara, don haka babu wanda ya gwada”, cewar Liu Guizhen, “kawai ina son samar musu mafita ne”.

Liu Guizhen da maigidanta, Yang Hongsheng, sun jagoranci shukar a wuri mafi dacewa a bakin kogi. Bayan shekaru 2 suna kula da shukar, iccen ya girma da kyau. Cikin lokacin bazara na 3 bayan shukar, Liu Guizhen ta sayar da wasu daga cikin itatuwan, kuma ribar da ta samu ya zarce wanda ake samu daga noman alkama da masara.

Nan da nan labarin nasarar Liu Giuzhen ya karade kauyen. Ta bi gida-gida domin tattaunawa da mutanen kauyen game da sana’ar, da kuma taimakawa masu sha’awa zabar wuri mafi dacewa da sayen irrai da taki.

Karkashin jagorancin Liu Guizhen, galibin mutanen kauyen suka fara shuka irin. A shekarar 2017, ta kafa wata kungiyar gama kai don inganta sana’ar, kuma ta fadada ta zuwa kauyuka makwabta.

Liu Guizhen ta yi iyakar kokarin kirkiro damarmakin kasuwanci ga ‘yan uwanta mutanen kauyen. Itatuwan magungunan gargajiya na tsirowa a kan duwatsu a fadin kauyen. Don haka ta karfafawa mutanen kauyen gwiwar hawa tsaunika don tsinko irin wadannan magunguna domin su sayar. 

Kudin shigar mutanen kauyen ya yi ta karuwa ta hanyar gwada abubuwa. Galibinsu sun sayi sabbin gidaje a gundumar, kuma sun fara rayuwa irin ta birni.

“Rayuwa za ta yi dadi da ma’ana idan ka yi kokarin taimakawa sauran mutane”, cewar Liu Guizhen, “Wannan ba gadon dabi’un iyalina ba ne kadai, wata ka’ida ce da na kafawa kai na. A kullum mahaifina na koya min tunawa da mutane a zuciyata, kuma na koyar da ‘ya’yana hakan ni ma.”

Yang Junyu, babbar diyar Liu Guizhen, ta taba aiki a matsayin nas a wani asibitin dake lardin Shandong na gabashin kasar Sin. Ta sha yi wa mahaifiyarta magiyar daukar hutu ta kai mata ziyara gidanta. Sai dai Liu Guizhen ba ta da lokacin hutu. Kuma ba za ta taba barin kauyen ba muddin ana bukatarta.

“Idan na tsaya a kan mumbari, to ni malama ce. A wajen aji kuma, ni likita ce. A matsayin daraktar kwamitin kauyen kuma shugabar reshen jam’iyyarmu a kauyen, zan rika tunawa da aminta da ni da jama’a suka yi da kuma nauyin dake wuyana”, kamar yadda Liu Guizhen ta fada.

Liu Guizhen ta karbi lambobin yabo da dama saboda irin kokarinta da jajircewa. (Kande Gao)